ABNA24 : Wannan dai na zuwa ne bayan da fadar shugaban kasar, ta sanar da cewa shugaban Trump, zai yi jinya a asibitin sojoji na tsawon wasu kwanaki masu zuwa, bayan gwaji ya nuna yana dauke da cutar korona.
Cikin wata sanarwa, sakataren yada labaran fadar, Kayliegh McEnany, ya ce Donald Trump wanda bai nuna alamu masu tsanani ba, yana nan lafiya kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa.
Da sanyin safiyar jiya Juma'a ne Trump ya sanar da cewa, shi da mai dakinsa Melania, sun kamu da cutar COVID-19, jim kadan bayan ya tabbatar da cewa wata hadimarsa dake da kusanci da shi ta kamu da cutar.
A halin da ake ciki dai shugabannin kasashen duniya daban daban na ci gaba da yi masa fatan samun sauki.
342/